Home DUNIYA Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ba zata lamunci ayyukan garkuwa...

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ba zata lamunci ayyukan garkuwa a jihar ba

Rundunar ‘Yan sandan jihar Kano ta sami nasarar ceto wata ƙaramar yarinya mai kimanin shekara biyu da rabi, bayan wani Makocinsu yayi garkuwa da ita harya nemi kuɗin fansar Naira Miliyan 2 a wurin iyayenta.
wannan na kunshe ta cikin wata sanarwar da Jami’in hulda da Jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, inda tace, tuni wanda ake zargin ya amsa laifin sa harma ya kai Jami’an rundunar wurin da ya ɓoye yarinyar.
Lamarin ya faru ne unguwar Sabuwar Gandu Kwarin Barka dake ƙaramar hukumar Kumbotso, inda matashin me suna Zakariyya Muhammad ɗan kimanin Shekaru 22 ya sace yarinyar me suna Amina.
Haka kuma rundunar ta kai yarinyar Asibitin ƙwararru na Murtala Muhammed dake Kano, inda aka bata kulawar gaggawa wanda tuni aka sallame ta.
Kwamishinan ‘yansandan jihar CP Salman Dogo Garba ya ce rundunar ba zata lamunci irin waɗannan ayyukan ba, a inda ya jaddada cewa zasu saka ƙafar wando ɗaya da masu yunƙurin aikata muggan laifuka a jihar.
daga bisani rundunar ta yaba da yadda al’ummar jihar suke bin doka da oda, harma ta buƙaci mutane su ci-gaba da sanya idanu a yankunan su domin bada gudunmawar kakkaɓe dukkan wasu ɓata gari a fadin jihar.
PRNigeria hausa
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp