Tinubu ya kafa sabuwar ma’aikatar harkokin kiwo a Nijeriya

Shugaban kasa Asiwajo Bola Ahmad Tinubu ya kafa sabuwar Ma’aikatar Harkokin Kiwon Dabbobi a Nijeriya.

wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsaka da rikici a zauren majalisar kasar kan yadda makiyaya zasu gudanar da harkokin kiwo a kasar.

Bola Tinubu ya sanar da hakan ne lokacin da ya ke kaddamar da kwamitin da zai gyara tsarin kiwo, Kwamitin da zai yi aiki wajen magance matsaloli tsakanin manoma da makiyaya,

A taron da ya sami halartar, mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, da kuma wasu jami’an gwamnati.

A watan Satumban 2023, Shugaba Tinubu ya amince da kafa kwamitin shugaban ƙasa don gyaran bangaren kiwo da magance rikice-rikicen makiyaya da manoma.

Wannan shawarar ta biyo bayan rahoton taron kasa kan gyara tsarin kiwo da rage rikice-rikicen da ke da nasaba da kiwo a Najeriya.
Kungiyar Miyetti Allah ta MACBAN, ta buƙace shugaban ƙasa ya ƙirƙiro ma’aikatar kiwo.

Shugabansu, Alhaji Baba Usman Ngelzarma, ya ce makiyaya na buƙatar ma’aikata mai zaman kanta da za ta kula da dukkanin al’amuran da suka shafi kiwo.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 9 hours 41 minutes 0 second,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 11 hours 22 minutes 25 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com