Hukumar kidaya ta Nijeriya (NPC) ta ce ta shirya tsaf domin gudanar da ayyukan kidayar AL’umma da gidaje, sai dai kawai tana jiran umarnin shugaban kasa Bola Tinubu ne domin ya amince da ranar da zaá fara.
Read Also:
shugaban hukumar ta NPC Malam Isa Kwarra ne ya bayyana hakan a makon daya gabata a yayin wani taro da aka gudanar a birnin tarayya Abuja domin zagayowar ranar kidaya ta duniya, wadda aka warewa ranar 11 ga watan yunin ko wacce shekarar.
Ya ce majalisar dinkin duniya ta ayyana dukkan bayan shekaru 10 a gudanar da kidayar, wannan ne yasa hukumar ta shirya gudanar da kidayar tun a watan Nuwamban 2020 wannan shine shirin su tun da fari.
da yake bayyana muhimmancin kidayar, Kwarra ya ce zata taimaka matukawa mahukunta wajen sanin cikakkan bayanin da kuma adanin al’umar dake rayuwa a kasa.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 23 minutes 27 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 4 minutes 52 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com