Kamfanonin jaragen Sama da ke saba ka’idoji za su fuskanci hukunci mai tsanani – NCAA

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya, NCAA ta yi gargaɗin cewa za ta hukunta kamfanonin sufurin da ke yaudarar matafiya a kan lokacin tafiyar jirage.

Mukaddashin daraktan hukumar, Chris Najomo ne ya bayyana hakan inda ya ce hukumar ba za ta lamunci rashin cika alƙawari da kuma kiyaye ƙa’idojin sufurin jirgin sama ba.

Ya yi gargaɗin cewa kamfanonin da suke saba ka’idojin za su fuskanci hukunci mai tsanani, kamar yadda doka ta yi tanadi.

Hukumar ta ce ta yi tanadi mai inganci domin sauƙaƙe yadda ake mallakar lasisin gudanar da kamfanonin jiragen sama a Najeriya, da kuma kaucewa kura-kuran baya.

“NCAA ta na fatan ganin hakan zai sa kamfanonin jiragen su tashi tsaye domin gudanar da ayyukan su yadda ya dace” inji Chris Najomo.

NCAA ta jaddada cewa babu wani dalili da zai hana kamfanonin jiragen sama gudanar da ayyukan cikin tsari kamar yadda ake yi a sauran ƙasashen duniya.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 12 hours 40 minutes 21 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 21 minutes 46 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com