Majalisar wakilan Nijeriya ta kafa kwamiti domin bincikar hukumar jin dadin alhazai ta kasar, bisa yadda ta gudanar da ayyukan hajin shekarar 2024.
Wannan dai na zuwa ne bayan kudirin da dan majlisar mai wakiltar al’ummar mazabar Barutai/Kaigama, Muhammad Bio daga jihar Kwara ya gabatar a gaban majalisar yayin zamanta na ranar talata.
Read Also:
biyo bayan kudirin majalisar tayi fatali da yadda hukumar ta kasa da kuma ta birnin tarayya Abuja ta gudanar da aikin hajjin na shekarar 2024, don haka ta kafa kwamitin da zai bincika wakilan hukumar a hajjin.
tuni dai kakakin majalisar wakilan Tajuddeen Abbas, ya ayyana mamba dake wakiltar Alúmmar mazabar Jibia/kaita daga Jihar Katsina, Sada Soli matsayin shugaban kwamitin.
an yi wa kudirin take, ” gaggauta bincike akan hukumar jin dadin alhazai ta NAHCON ta kasa da kuma ta birnin tarayya Abuja, Wakilansu, bisa birinburin a shirin gudanar da ayyukan sauke farali na shekarar 2024,”
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 30 minutes 47 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 12 minutes 12 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com