Home DUNIYA Sojojin Nijeriya sun kama masu garkuwa da mutane 3 a jihar Taraba

Sojojin Nijeriya sun kama masu garkuwa da mutane 3 a jihar Taraba

Sojojin Nijeriya karkashin dakarun Operation WHIRL STROKE (OPWS) sun sami nasarar tarwatsa maboyar ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa a tsaunin Adamu Katibu dake karamar hukumar Lau ta jihar Taraba.

Wannan na matsayin matakin da rundunar ke dauka na kawar da ayyukan ta’addanci da suka addabi sassan kasar.

atisayen ya gudanane bayan wasu bayanan sirri da dakarun suka samu, hadin gwiwa da wasu dakarun tsaro a kasar, kan maboyar ta ‘yan ta’addan a yankin, inda suka yi musayar wuta daga bisani wasu cikin su suka tsere.

sai dai dakarun sun sami nasarar kame ‘yan ta’adda uku daga cikin su, wadanda suka hadar da Haruna Buba mai kimanin shekaru (20), Hassan kakale mai shekaru da Hussaini kakale dukkansu masu shekaru (28) da haihuwa.

a yayin atisayen dakarun sun sami nasarar kubutar da Hauwa’u Alhaji Umaru da kuma Asma’u Alhaji Umaru da suka yi garkuwa da su tun a ranar 7 ga watan Yunin 2024, wanda tuni an kai su shalkwatar dakarun sojin dake ta 6 Brigade domin duba lafiyar su inda daga bisani za’a mika su ga ahlinsu.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp