Aƙalla ɗalibai 16 ne suka mutu bayan ruftawar ginin mai hawa biyu a wata makaranta a birnin Jos na jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya ranar Juma’a da safe.
Rahotonni sun ce ɗalibai masu yawa ne suka jikkata, yayin da ɗaliban da malamai suka maƙale a cikin ginin.
Ginin na makarantar Saint Academy – da ke unguwar Busa-buji a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa – ya rufta ne a lokacin da ɗaliban ke ɗaukar darussa.
Iyayen yara sun cika harabar makarantar bayan faruwar lamarin, domin sanin halin da ‘ya’yansu ke ciki, yayin da waɗanda suka ga gawarwakin ‘ya’yansu suka kiɗime.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya (NEMA) na ci gaba da aikin ceto domin zaƙulo sauran mutanen da ginin ya danne.
Kawo yanzu an gano gawargwaki aƙalla 16, to sai dai har yanzu ba a san adadin mutanen da suka mutu ba.
Akwai dai fiye da ɗalibai 1,000 a makarantar. Kawo yanzu dai ba a san dalilin da ya haddasa ruftawar ginin ba
Iyayen ɗalibai sun garzaya asibitin birnin Jos domin sanin halin da ‘ya’yansu ke ciki.
Likitoci na kira ga al’umma su bayar da gudunmowar jini domin ceto rayukan ɗaliban da aka kai asibitin.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 21 minutes 22 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 2 minutes 47 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com