Home DUNIYA An ceto mutum 4 cikin wadanda gini ya rufta kan su a...

An ceto mutum 4 cikin wadanda gini ya rufta kan su a Abuja

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na tabbatar da cewa wani gini mai hawa biyu ya rushe, tuni dai hukumomin ceto suka ce sun kuɓutar da mutum huɗu da ke karkashin bara guzai ginin

Lamarin ya auku ne a unguwar kubwa phase 2 da misalin karfe 7 na safiyar asabar.

Masu aikin ceto da jami’an tsaro na ci gaba da neman mutanen da ginin ya rufta da su.

Gidan ya rushe ne kwana ɗaya bayan wata makaranta ta rushe a jihar Filato, inda ya kashemutum 22 ya kuma raunata wasu 132.

Kwanaki 11 da suka wuce ma wani ginin ya rushe a unguwar Area 11 da ke yankin Garki a birnin Abuja.

An ruwaito cewa gidan tun da fari Otal ne mai suna Al-hilal, sai dai daga bisani aka mayar dashi gidan kwana.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp