Home DUNIYA Rundunar ‘yan sanda Nijeriya za ta fara amfani da fasahar zamani wajen...

Rundunar ‘yan sanda Nijeriya za ta fara amfani da fasahar zamani wajen rijistar motoci

Rundunar ƴan sandan Najeriya za ta fara amfani da fasahar zamani ta e-CMR wajen rijistar motoci a ƙasar nan da kwana 14.

Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fita, wadda tace  tsarin na e-CMR zai taimaka wajen inganta aikin jami’an ƴan sanda wajen gudanar da bincike da daƙile aikata laifuka ta amfani da ababen hawa, har ma da ayyukan ƴan bindiga da masu tayar da ƙayar baya.

Rundunar ta ce daga ranar 29 ga watan Yulin 2024, sabon tsarin mai amfani da na’urorin zamani, zai fara aiki domin inganta tsaro a sassan ƙasar.

Sanarwar ta ce sabon tsarin rijistar ababen hawan zai riƙa amfani da fasahar zamani wajen tattara bayanan kai tsaye na ababen hawa da waɗanda suka mallake su da kuma ayyukan da suke yi da su.

Hakan na nufin daga lokacin fara aiki da wannan sabon tsari, duk wasu sauye-sauye na takardun mota ko kuma wasu sassan motar za su gudana cikin sauki ba kamar yadda a baya ake ɗaukar lokacin haɗa irin waɗannan takardu ba.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp