Rundunar ƴan sandan Najeriya za ta fara amfani da fasahar zamani ta e-CMR wajen rijistar motoci a ƙasar nan da kwana 14.
Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fita, wadda tace tsarin na e-CMR zai taimaka wajen inganta aikin jami’an ƴan sanda wajen gudanar da bincike da daƙile aikata laifuka ta amfani da ababen hawa, har ma da ayyukan ƴan bindiga da masu tayar da ƙayar baya.
Rundunar ta ce daga ranar 29 ga watan Yulin 2024, sabon tsarin mai amfani da na’urorin zamani, zai fara aiki domin inganta tsaro a sassan ƙasar.
Sanarwar ta ce sabon tsarin rijistar ababen hawan zai riƙa amfani da fasahar zamani wajen tattara bayanan kai tsaye na ababen hawa da waɗanda suka mallake su da kuma ayyukan da suke yi da su.
Hakan na nufin daga lokacin fara aiki da wannan sabon tsari, duk wasu sauye-sauye na takardun mota ko kuma wasu sassan motar za su gudana cikin sauki ba kamar yadda a baya ake ɗaukar lokacin haɗa irin waɗannan takardu ba.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 12 hours 14 minutes 47 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 56 minutes 12 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com