Bincike: Shin da gaske ne Rundunar sojojin Nijeriya na da makarantar koyar da harkokin Muslinci?

IKIRARI: An yada wani hoto a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa runudunar sojojin Nijeriya na da makarantar koyar da harkokin addinin muslinci

CIKAKKEN LABARIN: Wani hoto da aka yada aka kafafar facebook wanda aka rubuta wasu kalamai masu cike da tambaya da ke cewa “da gaske ne?”  a hoton, akwai wasu manyan sojojin dake sanye da kayan aiki (uniform).

Wallafar ta jawo kace-nace a sashen bayyana ra’ayi. Yayin da da dama suka bayyana rashin gamsuwarsu, in da suke cewa kawai masu son tada tarzoma ne, duba da irin halayyar rashin yadda da juna a fannin addini da kabilanci, ya yin da wasu da dama suka fara nuna yatsa ga ‘yan siyasar yankin arewacin kasar.

In da wani kuma yayi rubutun cewa ai runudunar sojin na da irin wannan makaranta ta addinin kirista wadda ke taimakawa wajen ganin ta sanya dakarun sojojin bisa layin kyakkyawar dabi’a.

BINCIKEN SAHIHANCIN IKIRARI: domin tabbatar da ingancin ikirarin tawagar bincike sahihancin labara ta PRNigeria ta kira mai Magana da yawun rundunar sojin Janal Onyema Nwachukwu.

Janal Onyema Nwachukwu da wurwuri ya ce wannan labari ne na karya, kawai mutum ya yi tunanin cewa rundunar sojojin Nijeriya gudanar da wata makaranta ta koyar da harkokin addinin muslinci, a kuma yi watsi da sauran addinai. Ya kara da cewa rundunar sojojin Nijeriya hukuma ce ta kasar da ke da addinai wadda kuma take girmama ko wane addini.

Ya kara da cewa rundunar sojin Nijeriya na da makarantu da ke da alaka da addinai kamar ta harkokin addinin muslinci, akwai makaranta horon soji ta Protestanta a Yaba, akwai kuma horo ta Chaplain Catholic da Ojo.

Domin kara tabbatar da ingancin labarin sashen binciken sahihancin labarai na PRNigeria ya ziyarci shafin hukumar na X (twitter). Kuma bincike ya tabbatar da kalaman mai Magana da yawun rundunar sojin Janal Onyema Nwachukwu.

A cikin kalaman, rundunar sojojin Nijeriya ta musanta cewa tana wariyar addini, in da ta ce tana mutunta ko wannen, gami da bawa mabiya addinin damar gudanar da addinin musu cikin ‘yanci.

Haka kuma rundunar ta bayyana kudirin ta na muhimmanta ko wane addini, ta ce tana gudanar makarantu horo na addinin domin kara inganta addinin a cikin dakarunta, wanda suka hadar da makarantar horon ayyukan addinin muslinci, ta (Nigerian Army School of Islamic Affairs,) Makarantar horon soji ta Protestant, da kuma makarantar horo ta Nigerian Army Chaplain Catholic.

Wani binciken taswira (Map) da PRNigeria ta gudanar kan wuraren da makarantun horar da harkokin addinan suke. Army School of Islamic Affairs ta na Ikeja, makarantar horon soji ta Prostestan tana Yaba da Chaplain Catholic tana Ojo.

KAMMALAWA: PRNigeria  ta yanke hukuncin cewa ikirarin dake cewa rundunar sojin na gudanar da makaranta da ta shafi harkokin addinin Muslinci, ba tare da sun ambaci sauran makarantun da suka hadar da Protestant da Catholic a matsayin wata bukata ta son haifar da wani rikici cikin al’umma.

 

By PRNigeria

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1462 days 9 hours 22 minutes 39 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1444 days 11 hours 4 minutes 4 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com