Kungiyar marubuta labarin wasanni ta kasa reshen jihar Kano (SWAN) ta ja hankalin gwamnatin jihar da ta sanya kwararrun mutane dake da ilimi a fannin wasanni wajen jagorantar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars dama sauran harkokin wasanni, domin inganta harkokin wasanni a jihar.
Wannan na cikin wani sanarwa da kungiyar ta fitar ta bakin shugaban kungiyar na jiha wanda sakataren ta Zaharaddini Sale da Muhammad Nura Tijjani suka sanya wa hannu.
Kungiyar tayi kira da gwamnati ta gaggauta gyara da kuma daga likafar filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata yayin da ta bukaci gyara da kwaskware filin wasa na Mahaha duka domin inganta harkokin wasannni a jihar.
Kungiyar tace dole a kalli filin wasan gargajiya na Ado Bayero Square domin bashi fifiko kasancewar yanzu duniya ta juya kan inganta wasannin gargajiya domin farfado da al’adun al’umma.
Read Also:
a yunkurinta na inganta harkokin wasanni a jihar kano SWAN ta fitar da jadawalin kwamitin kwararru da masu bada shawara bisa cikakken tsari domin tabbatar da cigaban harkokin harkokin wasanni a jihar musamman abin da ya shafi kungiyar Kano pillars.
kazalika kungiyar ta yi Allah wadai da yanayin da kano pillars ta tsinci kanta a ciki,”mun fahimci halin da kungiyar ke ciki kuma muna tare da su wajen warware matsalolin kama daga kan yan wasa, shuwagabanni da kuma masu horarwa.
“Don haka muna kira da gwamnati ta hada kai da duk masu ruwa da tsaki domin kawo karshen matsalolin da kuma inganta harkokin wasanni a jihar.
idan za’a tuna kungiyar ta Pillars ta fuskanci matsaloli a baya bayannan wanda hakan ya haddasa rabuwar kan jagororin kungiyar gida biyu.
sa idai zuwan sabon kwamishinan wasanni a jihar Mustapha Rabi’u Kwankwaso yayi yunkurin kawo sauyi wanda ya sa aka samu sabon mai horarwa a kungiyar.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 20 minutes 55 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 2 minutes 20 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com