Home DUNIYA Tinubu ya ba kowanne Gwamna shinkafa tirela 20 a raba wa talakawa

Tinubu ya ba kowanne Gwamna shinkafa tirela 20 a raba wa talakawa

Gwamnatin Tarayya ta ayyana raba shinkafa tirela 20 ga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja, domin rabawa ga mabukata.

Za a raba kayan abincin ne a faɗin kasar a masatyin wani matsaki na kawar da matsalar yunwa da ke addabar kasar.

Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan ga manema labaran fadar Shugaban Kasa a ranar Litinin, jim kadan bayan fitowa daga taron Majalisar Zartawa wanda Shugaban Kasar, Bola Tinubu ya jagoranta.

Ministan ya ce majalisar ta fahimci yadda matsalar karancin abincin ke addabar ’yan kasar, don hakan ta amince da raba shinkafa tirela 20 ga kowacce jiha da Abuja ga mabukata.

Al’ummar Nijeriya dai na fama da matsalar tsadar abinci, abin da suka alakanta da cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi.

Matakin dai ya haifar da tashin farashin kayan masarufi da kayan amfanin yau da kullum a kasar da ke da arzikin man fetur da ma’adinan a karkashin kasa.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp