Home DUNIYA ‘Yan ta’adda sun yi garkuwa da mutane 150 tare da kashe 4...

‘Yan ta’adda sun yi garkuwa da mutane 150 tare da kashe 4 a jihar Zamfara

Rahotannin daga jihar Zamfara na bayyana cewa ‘yan taádda masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa sun yi garkuwa da mutane 150 cikin su har da yara kanana a kauyen Dan isa dake karamar hukumar kaura Namoda dake jihar.

harin ya faru ne makwanni kadan bayan da ýan bindigara suka saki mutune 46 mazauna garin Dogon kade da suka saka bayan an biya kudin fansa naira miliyan 21.

dan isa dai gari ne dake da nisan kilomita 14 zuwa birnin jihar wato gusua.

jaridar Emergency Digest ta ruwaito wani mazaunin garin da aka yi garkuwa da matarsa da dan Sa na tabbatar da aukuwar lamarin.

mutumin wanda ya bukaci a sakaye sunansa, ya ce ‘yan ta’addan sun tasamma garin ne kan babura kusan 150, kowannen su dauke da mutane uku, inda suka fara harbi a iska, abinda ya sa wasu cikin al’umma guduwa domin neman tsira.

“Matata, Na’imah da Da na dan watanni shida a duniya, Sudais, na cikin wadanda ”Yan ta’addan suka yi garkuwa da su, sai matar kanina, Aisha, da yaron ta dan watannin takwas, mata da yawa da kananan yara ýan binidgar sukayi garkuwa da su,” a cewar sa.

wani mzaunin garin Muhammad Auwal (ba sunansa na gaskiya kenan ba), ya ambaci cewa Hajiya Rakiya, matar Wamban Dan Isa, Alhaji Bello Halilu, da wasu mata ‘yan taáddan suka raunata a gidan Alhaji Halilu.

Aminu Bello Dan isa, wani mazaunin garin ya ce gungun ‘yan ta’addan dake karkashin dan bindiga Alhaji Shehu Bagiwa.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp