Gwamnatin tarayya za ta fara bayar da bashin karatu ga manyan makarantun gwamnatin tarayya kasar da suka nemi bashin nan da mako mai zuwa.
Sai dai shugaban asusun, Akintunde Sawyerr, ya ce ɗaliban makarantun da za su fara sabon zangon karatu ne kawai za su ga kuɗin a asusunsu a yanzu.
A jiya Laraba ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙaddamar da asusun mai suna Nigerian Education Loan Fund (Nelfund) a hukumance a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Read Also:
Mista Sawyerr ya ce jimillar ɗalibai 170,000 ne suka yi rajista da asusun, waɗanda suka ƙunshi ɗaliban jami’a, da na kwalejojin ilimi da fasaha.
“A taƙaice dai, jimillar ɗalibai 110,000 ne suka nemi bashin. Sun ba da bayanansu tare da miƙa takardun neman, kuma su ne suka cancanta. Amma duk da haka za mu ƙara gudanar da bincike a kansu… Amma da alama sama da mutum 110,000 ne za su fara samun bashin a sati mai zuwa,” in ji shi.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 10 hours 28 minutes 21 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 12 hours 9 minutes 46 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com