Ƴan majalisar wakilan Najeriya sun amince da a zabtare kaso 50 na albashinsu na tsawon watanni shida a wani mataki na nuna tausayawa ga yanayin matsin tattalin arziƙi da yunwa da ƴan Najeriya ke ciki a halin yanzu.
Wannan dai ya biyo bayan amincewa da gyaran ga buƙatar da mataimakin shugaban majalisa, Benjamin Kalu ya yi na buƙatar ƴan majalisar da su sadaukar da kaso 50 na albashin nasu na naira 600,000 da suke karɓa.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Hon Benjamin Kalu ya ce zabtare albashin nasu zai taimaka wa gwamnati wajen sauƙaƙa wa ƴan ƙasar rayuwarsu.
Hakan na nufin ƴan majalisar wakilan guda 360 za su tara tsabar kuɗi har naira miliyan 648 wato fiye da rabin naira biliyan ɗaya, idan aka zabtare musu naira miliyan 108 a duk wata.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da naira 70,000 a matsayin sabon albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikatan gwamnatin ƙasar.
Tinubu ya sanar da sabon albashin ne a ganawarsa da wakilan ƙungiyoyin ƴan ƙwadago na ƙasar a ranar Alhamis.
PRNigeria Hausa











