Home General ‘Yan sanda a Nijeriya sun kama mutane 1,284 da ake zargi da...

‘Yan sanda a Nijeriya sun kama mutane 1,284 da ake zargi da laifuka

Rundunar ‘yan sandan kasar nan ta ce dakarunta sun sami nasarar kama mutane 1,284 da ake zargi da aikata mabambanta laifuka a cikin makwannin shidda da suka gabata.

Mai Magana da yawun hukumar na kasa Muyiwa dejobi ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a yayin da ake holen wadanda ake zargin da aikata laifuka daban daban.

Haka kuma yace daga cikin wadanda aka kama akwai mutum 307 da ake zargin su da aikata fashi da makami sai kuma 296 da ake zargi da aikata laifukan garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, sai kuma mutane 176 da ake zargi da laifukan fyade da tabargaza, ana kuma zargi mutane 301 da aikata laifukan kisan kai, sai kuma mutane 204 da ake zargin su da shiga kungiyoyin asiri.

Adejobi yace rundunar ta sami nasarar kubutar da mutane 97 da akayi garkuwa da su, inda suka sami nasarar kwato makamai 284 gami da alburusai 6,702.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp