Home General APC ta lashe kujerun shuwagabannin kananan hukumomi a jihar Ebonyi

APC ta lashe kujerun shuwagabannin kananan hukumomi a jihar Ebonyi

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta jihar Ebonyi, EBSIEC, ta bayyana jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaben kananan hukumomin jihar da ya gudana a ranar Asabar

Shugaban Hukumar Jossey Eze ya bayyana hakan a Abakaliki, inda ya ce jam’iyyar ta lashe dukkan kujerun Shugabancin Kananan hukumomi 13 da Kansiloli 171da ke jihar.

Eze ya ce jam’iyyun siyasa uku ne Suka shiga zaben, Wanda suka hada da jamiyyar APC, APGA da Kuma Labour Party.

Tuni dai shugaban hukumar zaben ya sanar da amincewar sakamakon.

Daga nan sai ya yabawa masu ruwa da tsakin na hukumar, da Kuma jami’an tsaro Kan yadda aka Sami nasarar gudanar da zaben lafiya.

PRNigeria Hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp