Kada kuyi zanga-zanga, zaifi a zauna a sasanta – Sunday Dare ga matasan Nijeriya

Tsohon Ministan wasanni da ci gaban matasa a gwamnatin Buhari, Sunday Dare ya shawarci matasan kasar nan a kan hanyar samun saukin halin da ake ciki.

Tsohon Ministan ya ce akwai wata hanya da za a bi a maimakon a tafi zanga-zangar gama gari da aka shirya za a yi na kwanaki 15.

A wata hira da tsohon Ministan ya yi ta shafinsa na X, ya ce har yanzu jama’a na kokarin farfado wa daga cikin halin da zanga-zangar endSARS ta jefa ‘yan Najeriya ba.

Tsohon Minista a gwamnatin Buhari, Sunday Dare ya gargadi matasa kan illar da zai iya biyo bayan zanga-zangar gama garin da suke shirin farawa.

ya ce akwai fargabar bata-gari za su iya shiga rigar masu zanga-zanga wajen tayar da hatsaniya a kasar nan.

Dare ya bayyana cewa kamata ya yi matasan kasar nan su zauna da gwamnati domin neman mafita.

Ya ce kamata ya yi a zauna, a tattauna da gwamnati a kan hanyar da ta fi dace wa wajen magance koken ‘yan kasa.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1255 days 29 minutes 22 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1237 days 2 hours 10 minutes 47 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com