Ƙungiyar kare haƙƙin Ɗan Adam, yaƙi da rashin adalci dama bibiya akan shugabanci na gari wato War Against Injustice (WAI), ta ce babu gudu babu ja da bayan akan Zanga-zangar da ta ayyana gudanarwa daga ranar 1 ga watan Agusta zuwa 10 ga wata.
Babban daraktan ƙungiyar Kwamared Umar Ibrahim Umar ne ya sanar da hakan ta cikin wani saƙon murya da jaridar GTR HAUSA ta samu a yammacin talata, inda ya ce matakin ya zama dole domin nunawa mahukunta halin da talaka yake ciki.
A cewar Kwamared Umar “Ina wannan magana ne a matsayin martani dangane da taron manema labaran da wata ƙungiya tayi a jiya wadda ta ce sun janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa, adan haka mu bamu janye ba kuma zamu gudanar a ranakun da muka ayyana.
Ya ƙara da cewa zasu gudanar da zanga-zangar tasu cikin lumana da kwanciyar hankali kuma ba tare da taɓa haƙƙin al’umma ba, ta yadda zasu nunawa duniya halinda talakawan ƙasar ke ciki na yunwa, fatara da kuma talaucin da yayi musu katutu.
A ƙarshe ƙungiyar tayi fatan Al’ummar jihar zasu basu haɗin kai da goyon baya domin ayi lafiya kuma a kammala lafiya.
A jiya ne ƙungiyar Shugabannin Matasan Arewacin Najeriya ta ce ta janye zanga-zangar da ta shirya gudanarwa, a sakamakon yadda ta gano akwai masu ƙoƙorin rikita ƙasar ta hanyar amfani da zanga-zangar tasu.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 20 hours 40 minutes 20 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 22 hours 21 minutes 45 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com