Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya jaddada aniyar sa ta samawa dakarun ‘yan sandan kasar makamai da daukar’ karin jami’ai domin yaki da laifuka a kasar.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin gudanar da bikin kaddamar da sashen yaki da laifukan internet a binrin tarayya Abuja ranar laraba, inda ya bayyana manufarsa ta kawo karshen ayyukan hadakar jami’an tsakanin hukumomi a kasar.
Read Also:
Yace ya fahimci laifukan zambar kafar Internet ya kara karuwa a kasar, yace abu ne da baya bukatar hadin gwiwa tsakanin hukumomin domin magance matsalar.
Da yake jawabi a wajen taron Shugaban kasa Bola Tinubu wanda ya sami wakilcin ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Bossum Tijani, yace yanayin tsaro a kasar yayi tsamari lamarin dake bukatar sake zage dantse domin magance matsalar.
Tinubu ya tabbatarwa da Al’ummar Nijeriya cewa gwamnatinsa zata yi dukkan mai yiwuwa wajen sanya makudan kudi don gani ta samawa jami’an ‘yan sandan makamai
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 6 hours 31 minutes 31 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 8 hours 12 minutes 56 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com