Na dauki dukkan wani laifin da gwamnatin dana gada tayi – Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa dukkan masu rura wutar sai an yi shirya zanga-zangar tsadar rayuwa ba masu kaunar cigaban kasar bane.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da malamai, a wani bangare na ganawa da yake da rukunonin mutane a kasar domin tabbatar da ya gamsar da ýan Nijeriya aniyarsa ta magance matsalolin dake addabar Al’ummar kasar.

Ta cikin wata sanrwa da mai Magana da yawun shugabn kasar Ajuri Ngelale ya fitar, ta ambaci tinubu na cewa “Masu Daukar nauyin zanga-zangar ba sa kaunar kasarmu. Basa kaunar alúmma. Suna da shaidar zama a wasu kasashen,” inji Tinubu.

Ko da yake bai bayyana wani wanda ya dauki nauyin wannan zanga-zangar ba, amma ya ce wadanda ke fafutukar sai an yi zanga-zangar suna da fasfo na daban da idan al’amura sun dagule a kasar suna da kasar da zasu koma.

Shugaba Tinubu ya bayar da hujjar cewa zanga-zangar an shirya ta ne cikin fushi da kiyayya, kuma idan ba a yi a hankali ba za ta iya rikidewa zuwa tashin hankali da mayar da kasar baya.

Ya ci gaba da cewa shi ya dauki nauyin yakin neman zaben sa tun da farko, don haka bashi da wani mutum ko kungiya da take juya shi ko ta fada masa yadda zai tafiyar da gwamnatinsa.

A nasa jawabin shugaban tawagar malaman Sheikh Bala Lau ya godewa shugaban kasar, Sannan ya yi alkawarin za su cigaba da yi masa addu’a da ba shi goyon baya da kuma wayar da akan al’umma.

”Zaman Lafiya shi ne komai a rayuwar al’umma, saboda zaman Lafiya da taimakon Allah Annabi Ibrahim ya fara roka a wajen Allah” a cewar Sheikh Bala Lau

Da yake ganawa da Sarakunan Gargajiya Shugaba Bola Tinubu ya fada masu cewa gwamnatinsa ta himmatu sosai wajen ganin ta magance matsalolin da kasar ta ke fuskanta.

”Babu shakka ni na nemi shugabancin kasar nan, lallai na zo gare ku don neman hadin kai da goyon bayanku, don haka ba ni da wani uzuri da zan nema, illa in tsaya na yi aiki tukuru don magance matsalolin da yan kasa su ke fuskanta”. A cewar Tinubu

”Na dauki duk wani laifi da gwamnatin da na gada ta yi, kawai abun da yake gabana shi ne yadda zan ciyar da Nijeriya gaba “. Inji Tinubu

Ya ce yana aiki ba dare ba rana domin ganin yan Nijeriya sun sami jin dadi, yace shi yasa ya fara daukar matakai na matso da gwamnati kusan da al’umma, daga cikin su akwai batun baiwa kananan hukumomi yancin cin gashin kansu.

 

PRNigeria Hausa

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 12 hours 30 minutes 28 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 11 minutes 53 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com