Shugaban ƙasar China Xi Jinping, ya gayyaci takwaransa na Najeriya Bola Tinubu, domin kai ziyarar aiki ƙasar.
Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar, wadda ta ce mataimakin ministan ƙasashen wajen China, Chen Xiaodong, ne ya je da saƙon gayyatar ca wata ziyara da ya kai Najeriya.
Mista Xiaodong ya yaba wa Shugaba Tinubu kan irin tsare-tsarensa, da irin rawar da shugaban ke takawa a matsayinsa na jagoran kungiyar Ecowas.
“Kai shugaba ne mai haƙaza da fikira. Mun yi imanin cewa ganawar ka da Mista Jinping zai kawo damarmaki masu yawa ga Najeriya da Afirka,’’ in ji shi.
A nasa ɓangaren shugaban na Najeriya ya yaba wa shugaban China, bisa ƙoƙarin da yake yi na ƙarfafa alaƙa da Najeriya da ƙasashen nahiyar Afirka.
“Mun yi imani da alaƙar da ke tsakaninmu, kuma muna son yauƙaƙa danƙon zumuncin da ke tsakaninmu , musamman ta hukumomin MDD da ƙungiyar BRICS da G20.”, in ji sanarwar.
Haka kuma shugaban ya yaba da saƙon gayyatar da shugaban na China ya aika masa na ziyarar aiki zuwa China.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 9 hours 42 minutes 51 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 11 hours 24 minutes 16 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com