Home General ”Arewa Media Writers” ta umarci mambobinta su fito Zanga Zanga

”Arewa Media Writers” ta umarci mambobinta su fito Zanga Zanga

Ƙungiyar Marubutan Arewa a Kafofin sadarwa na zamani wato Arewa Media Writers, ta umarci dukkan Mambobinta na Jihohi 19 har da Abuja su fito Zanga-zangar lumana a ranar Alhamis 1 ga watan Augusta.

Ƙungiyar ta sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan yaɗa labaranta na ƙasa Muhammad Kwairi Waziri ya aiko wa manema labarai a safiyar yau Litinin. inda ta ce ya zama wajibi su fito domin ƙara sanar da gwamnati matsalolin da ake fuskanta a yankin Arewa.

Sanarwar ƙungiyar ta ƙara da cewa al’ummar Arewa suna cikin matslolin rashin tsaro, yunwa, tsadar rayuwa, amma kuma gwamnati ta kasa magance musu matsalolin.

Haka zalika ƙungiyar ta ƙara jaddada wa magoya bayanta cewa babu fitowa da makami ko cin zarafin wani, ko ɗaukar kayan wani a yayin zanga-zangar, wanda dama ba fito na fito za’ai da gwamnati ba, illa kira ga hukuma da su san halin matsi da ƙuncin da al’umma suke ciki.

A ƙarshe ta yi kira ga dukkan masu fitowa zanga-zangar da su bawa jami’an tsaro haɗin kai yayin fitar, kuma su kula da bin doka da oda ta ƙasa Nijeriya.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp