Gwamantin Nijeriya ta umarci Jami’oin kasar da su Tabbatar da tsaron Lafiyar dalibai da kuma maáikata a makarantunsu yayin da ake gudanar da zanga-zangar.
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da mukaddashin shugaban hukumar kula da jami’oin kasar, Chris Maiyaki ya fitar wacce aka rabawa manema labarai a yau Litinin bias umarnin ministan ilimin kasar Farfesa Tahir Mamman.
Read Also:
Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da matasa a Nijeirya ke shirin fitowa titinu domin nuna bakin ciki da haln kuncin rayuwa da suke ciki a kasar, dake da arzikin man Fetur da tarin ma’adanai.
Ta cikin sanarwar Ministan ya kuma bukaci dalibai da su kasance a makarantunsu tare da mayar da hankali ga karatunsu domin kaucewa fadawa hatsari a yayin zanga zangar.
“Gwamnatin tarayya tana sane da hakkin da kowanne dan Nijeriya ke da shi wajen gudanar da zanga zangar lumana, amma mun damu da lafiyar ma’aikata da dalibai da makarantu a yayin zanga-zanga.
” A don haka minista ya umarci dukkan shugabannin makarantu da su dau matakai don tabbatar da tsaron dalibai da ma’aikatan jami’a”.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 6 hours 16 minutes 56 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 7 hours 58 minutes 21 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com