Home Labarai Jami’an tsaro sun yi arangama da masu Zanga-Zanga a jihar Kano

Jami’an tsaro sun yi arangama da masu Zanga-Zanga a jihar Kano

Wasu bayanai daga unguwar bachirawa a jihar Kano na bayyana cewa an yi arangama tsakanin matasan dake fakewa da zanga- zangar tsadar rayuwa suna fasa shaguna da dukiyoyin Al’umma a jihar da jami’an tsaro.

Matasan dai na kokarin kutsawa wani katafaren wurin sayar da kayan masarufi dana kwalam da makwalashe, wannan ne yasa dakarun ‘yan sandan daukar matakin dakile yunkurin nasu abinda ya kai ga harbin wasu daga cikin masu fakewa da zanga zangar.

Tun dai da sanyi safiya matasan suka fito domin sake dorawa daga inda aka tsaya a zangar da gwamnatin jihar ta dakatar da ita ta hanyar saka dokar hana fita, bayan ta zargi wasu manyan mutane a jihar da haifar da tarzoma a cikin ta.

Wakilin PRNigeria ya zaga yankin ya tattauna da wasu mutane da lamarin ya auku a gaban idon su, wanda suka ce har an sami asarar rayuka.

Mun yi kokarin tuntubar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa domin jin yadda lamarin yake, amma bai sami damar amsa kiran ba.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp