Shugaban Nijeriya Bola Tinubu zai yi jawabi ga Al’ummar kasar a ranar lahadi 4 ga watan agustan shekarar 2024 da muke ciki, wandake matsayin rana ta hudu da shiga zanga-zangar gama gari
Wannan dai na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai taimakawa shugaban na musamman kan harkokin yada labara Chief Ajuri Ngelale, wadda tace shugabn zai yi jawabin da karfe 7 na safiyar lahadi.
Read Also:
Za dai a saka hirar kai tsaye a kafafen yada labarai na gwamnatin tarayya da suka hadar da tv da radio, da suka hadar da NTA da gamayyar rukunin gidajen radio na tarayya wato FRCN.
Wannan dai na zuwa ne bayan da aka shiga rana ta uku da fara gudanar da zanga-zangar nuna halin da ake ciki na matsin rayuwa da talauci a kasar nan.
Zanga-zanagr dai na neman barin baya da kura, inda ta haifar da asarar rayuka kamar yada kungiyar Amnesty international ta bayyana a cikin rahoton ta.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 19 hours 45 minutes 42 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 21 hours 27 minutes 7 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com