Ƙungiyar kare haƙƙin dan Adam, yaƙi da rashin adalci dama bibiya akan shugabanci nagari wato War Against Injustice (WAI), ta bayyana shirinta na maka Gwamnatin Najeriya a Kotun ECOWAS nan bada jimawa ba.
Babban Daraktan ƙungiyar Kwamared Umar Ibrahim Umar ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa manema labarai a Lahadi, biyo bayan Jawabin da Shugaban ƙasar Bola Tinubu yayi wanda ya nuna rashin damuwa da halin da Talakawan ƙasar ke ciki.
A cewar sa “Dole mu ɗauki wannan mataki a sakamakon yadda Gwamnatin ta yi burus da buƙatun da Al’ummar ƙasar suka gabatar mata a wannan lokaci na zanga-zanga, harma Jami’an tsaro suke cin zarafin ‘yan ƙasar dama kashe su”.
Haka kuma ya buƙaci jami’an tsaro suyi gaggawar kama ‘yan Siyasar da suka ɗauki nauyin ɓata zanga-zangar, ta hanyar hayo ‘yan dabar da suka farwa dukiyar al’umma dama kayan Gwamnati.
Bugu da ƙari ƙungiyar ta yi Allah-wadai da cin zarafin ‘yan Jaridar da aka yi a lokacin zanga-zangar, suna tsaka da aikin su na hidimtawa al’umma dama ƙasar gaba-ɗaya.
A ƙarshe ƙungiyar ta yi fatan dukkan ɓangarorin da suke da alaƙa da matakin da suke shirin ɗauka zasu basu haɗin kan da ya kamata, domin nemowa waɗanda aka ci zarafin su haƙƙinsu dama hukunta dukkan masu hannu a cikin lamarin.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 15 hours 7 minutes 47 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 49 minutes 12 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com