Kungiyar War Against Injustice tayi Allah wadai da kasha mutane a wasu unguwannin jihar Kano, yawan wata arangama da dakarun tsaro a lokacin zanga-zanagr tsadar rayuwa a jihar.
Shugaban kungiyar Kwamared Umar Ibrahim Umar, ne ya bayyana hakan inda yace an hallaka mutane unguwannin na Kurna, Rijiyar Lemo, da Sharaɗa a jihar, da wasu sassan Najeriya.
Muna kira ga rundunar ‘yan sandan Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta binciki wadannan zarge-zarge tare da daukar matakin da ya dace kan masu aikata laifin.
Read Also:
Haka kuma muna kira ga masu ruwa da tsaki da su ba mu hadin kai wajen neman adalci ga wadanda abin ya shafa da iyalansu. Muna neman a ba da cikakken bayani kan rayukan da aka rasa da kuma jikkatar da aka samu a lokacin zanga-zangar.
Yin amfani da karfi kan masu zanga-zangar lumana cin zarafi ne da take hakkin bil’adama da ‘yancin walwala. Za mu ci gaba da bayar da shawarwarin kare wadannan hakkoki tare da neman a gurfanar da wadanda ke da hannu a wannan ta’asa.
Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda abin ya shafa tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.
PRNigeria Hausa