Gwamnatin Rasha ta nesanta kanta da wasu masu zanga-zanga a Najeriya waɗanda aka gani suna ɗaga tutar ƙasar Rasha.
A ranar Litinin an ga tuɗaɗowar ɗumbin masu zanga -zanga a jihohin arewacin Najeriya kamar Zamfara da Kaduna, inda wasu daga cikinsu ke ɗaga tutar Rasha.
Sai dai a wata sanarwa da aka sanya a shafin na intanet, ofishin jakadancin Rasha a Najeriya ya ce matakin da wasu masu zanga-zanga suka ɗauka na amfani da tutar Rasha mataki ne na ƙashin kansu, kuma wannan ba shi ne ainahin manufa da muradin ƙasar Rasha ba.
Sanarwar ta ce: “Kamar a kodayaushe, muna sake jaddada cewa Rasha ba ta shiga cikin harkokin cikin gida na ƙasashe masu ƴanci, ciki kuwa har da Najeriya.”
Rasha ta ce tana martaba mulkin dimokuraɗiyyar Najeriya kuma tana kyautata zaton cewa zanga-zangar da ake yi a ƙasar na kan doka da kuma tsari na mulkin demokuraɗiyya.
Sanarwar ta kammala da cewa “sai dai za mu yi Allah-wadai idan wannan zanga-zanga ta rikiɗe zuwa tarzoma.”
Dubban masu zanga-zanga ne suka hau kan titunan biranen Najeriya a zanga-zangar adawa da matsin rayuwa da al’ummar ƙasar ke ciki.
Zanga-zangar ta ci gaba a ranar Litinin bayan da ƙungiyoyin da ke jagorantarta suka ce jawabin da shugaban ƙasar ya yi a ranar Lahadi bai taɓo buƙatunsu ba.
An tsara gudanar da zanga-zangar ne tsawon kwana goma, daga 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 1 hour 5 minutes 4 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 2 hours 46 minutes 29 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com