Gwamnonin Nijeriya sun fara musanta Maganar biliyan 570 da Tinubu yace ya basu

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya musanta maganar da Shugaba Bola Tinubu na Nijeriya ya yi cewa gwamnatin tarayyar ƙasar ta bai wa jihohi, sama da naira biliyan 570, domin tallafa wa jama’a

A jawabinsa na neman kwantar da hankalin al’ummar ƙasar da ke zanga-zangar tsadar rayuwa da rashin shugabanci na gari, Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta raba kuɗin ga gwamnonin jihohin ƙasar 36 na ƙasar, domin sauƙaƙa wa jama’a matsin rayuwa.

Ƙari a kan waɗannan kudaden Shugaba Tinubu ya ce, gwamnatin tasa, ta kuma bai wa ƙananan harkokin kasuwanci 600,000 tallafi, sannan kuma akwai wasu ƙarin ƙananan sana’o’in 400,000 da za su amfana da tallafin su ma.

Ta cikin wani sako da Gwamnan na jihar Oyo, Seyi Makinde ya wallafa a shafinsa na X, a ranar Alhamis, ya ce shi dai jiharsa ba ta san da wannan kuɗi da Tinubun ya ce gwamnatinsa ta raba wa jihohi ba.

Gwamnan ya ce yana mayar da martani ne kan maganar da wani ɗan jihar tasa ya yi kan iƙirarin gwamnatin tarayyar cewa ta bai wa jihohi sama da naira biliyan 570 domin tallafa wa jama’a kan ƙuncin rayuwa.

Mista Makinde ya ce, maganar na daga irin batutuwan da gwamnatin tarayyar ke yi ne na faɗin abin da ba haka yake ba, yana mai ƙarin bayani da cewa: ” Kudaden da ake magana na daga cikin rancen bankin duniya na shirin NG-CARES, wanda kuɗi ne da ake tallafa wa jihohi wajen farfaɗowa daga annobar Korona, inda jiha za ta yi amfani da kuɗinta ta aiwatar da shirin, daga baya kuma bankin duniya ya mayar mata da kuɗin ta hanyar gwamnatin tarayya bayan bankin ya tantance abubuwan da jihar ta yi da nasarorin da ta samu.

Ya ce, ” Ya kamata ma fa a sani cewa kuɗin na bankin duniya bashi ne ga jihohi ba tallafi ba, saboda haka jihohi za su biya kuɗin.

Gwamnan ya ce jiharsa, Oyo, ta samu kuɗin ne, kashi biyu, inda a kashin farko aka ba ta naira biliyan 5.98, sannan a kashi na biyu ta samu naira biliyan 822.

”Saboda haka a taƙaice gwamnatin tarayya ba ta ba jihar Oyo wani kuɗi ba.

Makinde shi ne gwamnan jam’iyyar PDP, na biyu da ya soki Tinubu a kan jawabin a kwanakin nan.

Na farko shi ne Gwamna Bala Mohammed na Bauchi da ya ce jawabin shugaban soki-burutsu ne kawai – ko holoƙo ne – hadarin kaka.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 18 hours 5 minutes 9 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 19 hours 46 minutes 34 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com