Masu zanga-zanga sun bukaci Tinubu ya kori IG

Masu shirya zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya sun bukaci shugaban kasa Bola Tinubu daya gaggauta cire babban Sifetan ‘yan sandan kasar Olukayode Egbetokun, bisa zargin kisan masu zanga zanga tsadar rayuwa ta ”Endbadgovernance”.

Wannan dai na kunshe ta cikin wata sanarwa da kodinetan kungiyar ”take it back movement” Sanyaolu Juwon ya fitar, inda ta zargi jami’an ‘yan sanda kasar nan da hallaka masu zanga-zanga akalla 40 a lokacin da ake gudanar da ita kasar.

Haka kuma kungiyar tace jami’an sun tsare akalla mutane dubu 1 dake zanga-zanga kan tsadar rayuwa a wasu jihohin kasar nan. Don haka ya zama wajibi shugaban kasa ya kori babban sifeton ‘yan sandan bisa alhakin hallaka mutuane 40 wadanda aka harbe da alburushi a kokarin su na inganta laumar da zasu kai baka.

Kawo yanzu dai mutane dubu daya rundnar ‘yan sandan kasar na ke tsare da su, inda dakarun ke tsare da mutane 632 a jihar kano inda suka kama mutane 109 a jihar sokoto a gidajen ajiya da gyaran hali.

Ko da yake daai a iya cewa zanga-zangar ta dauki wani salo musamman a wasu jihohin arewacin kasar inda a safiyar wannan rana ake gudanar da salloli da addu’oin alkunutu, domin magance tsadar rayuwa a fadin kasar.

 

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 6 hours 8 minutes 8 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 7 hours 49 minutes 33 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com