Zan-Zanga – An jibge Jami’an tsaro a wasu biranen Nijeriya bisa tattakin mutum miliyan daya

An jibge jami’an tsaro a wasu manyan biranen kasar nan biyo bayan tattakin mutane miliyan daya da masu shirya zanga-zanagr tsadar rayuwa ta endbadgovernance, sukayi a yauy asabar.

Masu zanga zangar sun ware kwanaki 10 wanda ake zaton tazo karshe a wannan rana, zanga-zagar da ta bar baya da kora, bayan da aka zargi jami’an tsaro da hallaka mutane masu tarin yawa a lokacin da ake tsaka da gudanar da ita.

Tun da fari dai matasan sun bukaci gwamnatin kasar nan ta gaggauta damo da tallafin man fetur data cire tare kuma da mayar da mafi karancin albashi zuwa naira dubu 250 gami da kawo karshen gudanar da mulki ba yadda ya kamata ba.

Sai dai zanga-zangar ta haifar da hargitsi a wasu jihohi da suka hadar da Kano, Kaduna, rivers da kuma jihar Bauchi.

Amma dai masu zanga-zangar sun shirya rufe kasar nan a ranara Asabar domin bayyana bukatun su, bayan sun bayyana jawabin Bola Tinubu na ranar lahadin data gabata a matsayin abinda bai gamshe sub a.

Kasr nan dai na fama da matsalar tsadar kayan masarufi, tun bayan da gwamnatin tarayya ta janye tallafin man fetur ga kuma matsalar tsaro da iya cewa gwamantin ta gada daga Gwamnatocin baya.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 6 hours 15 minutes 9 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 7 hours 56 minutes 34 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com