Hukumar da ke Kula da Matasa Masu yi wa Kasa Hidima (NYSC) ta ce ba ta umarci matasa masu hidimar ƙasa su gyara asusun ajiyarsu na bankuna domin ta fara biyan su N70,000 ba.
NYSC dai a yanzu haka tana biyan matasan Naira 33,000 a kowanne wata a matsayin kuɗaɗen alawus-alawus.
Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Daraktanta na yaɗa labarai, Eddy Megwa, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
A cewar sanarwar, yanzu haka kururuwar na nan ta karaɗe shafukan sada zumunta na zamani, inda ta ce amma ƙarya ce tsagwaronta.
Read Also:
Eddy ya kuma ce, “Muna sanar da matasa masu yi wa ƙasa hidima, iyaye da sauran jama’a cewa har yanzu ba mu karɓi umarni daga sashen gwamnati da ke kuka da batun biyan albashi ba a kan lamarin.
“Saboda haka, ba zai yiwu NYSC mu bayar da wani umarni ba a kan lamarin.
“Matasa masu yi wa ƙasa hidima sun san hanyoyin da muke bi idan za mu fitar musu da sanarwa, don haka su yi watsi da wannan maganar.
“Daga wannan sanarwar, muna ba matasan shawara da su daina yarda masu neman tayar da zaune tsaye suna wasa da hankulansu,” in ji shi.
A ƙarshen watan da ya gabata ne dai Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu a kan sabuwar dokar mafi ƙarancin albashi wanda yanzu ya koma Naira 70,000.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 28 minutes 1 second,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 9 minutes 26 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com