Dangote ya musanta kayyade farashin Man fetur

Shugabannin matatar man Ɗangote sun yi watsi da rahotannin da ke cewa an ƙayyade farashin man fetur a kan naira 600 kan kowacce lita, inda ta bayyana rahotannin a matsayin jita-jita marar tushe.

A wata sanarwa da babban jami’in kula da harkokin kasuwanci da sadarwa na rukunin kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina, ya fitar a shafin sada zumunta na X, ya yi tsokaci kan jita-jitar da ake ta yaɗawa da ke cewa matatar na tattaunawa da ƙungiyar dillalan man fetur ta ƙasar IPMAN, a kan yadda za a cimma matsaya wajen sayar da man a kan naira 600 kan kowacce lita.

Kamfanin ya fayyace cewa bai ƙulla wata yarjejeniya da ƙungiyar ta IPMAN ba, ya kuma jaddada cewa duk wani mataki da kamfaninsu ko matatar za ta ɗauka za a sanar a hukumance.

Sanarwar ta cewa “An jawo hankalinmu kan labarin da ke cewa kamfanin Dangote ya ƙayyade farashin man fetur kan naira 600 kan kowace lita, a jiya Talata, 13 ga watan Agustan 2024.”

“Za mu so mu fayyace cewa ba mu da wata alaƙar kasuwanci da IPMAN a yanzu.”

Ya ce “Ba mu taɓa tattaunawa kan farashin man fetur da IPMAN ba kuma ba su da wani hurumin yin magana a madadinmu.”

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1255 days 41 minutes 9 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1237 days 2 hours 22 minutes 34 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com