Hukumar bada agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA tace ambaliyar ruwa ta shafi mutane 227,494, inda ta lalata gidaje 32,837 a jihohi 27 dake fadin kasar.
Haka kuma sanarwa da NEMA ta fitar tace ambaliyar ta lalata kadada kimanin 16,488 na gonaki da tuni sun fara fitar da amfani
Read Also:
Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Ezekiel Manzo ya fitar a ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja, sanarwar ta ambaci babban daraktan hukumar, Zubairu Umar na cewa hukumar zata cigaba da sanya idanu da kuma wayar da kan al’ummar kan matsalolin toshe magudanan ruwa da hanyoyin wucewar sa.
Umar ya shawarwa hukumar bayar da agajin gaggawar ta jihohi da shuwagabannin al’umma da su shiryawa daukar mataki kan samun yawaitar abaliyar ruwan anan gaba, sannan kuma ya ce kada manoma su damu bisa kamfar rashin ruwa, zai zo karshe kamar yadda hasashen NiMet ya bayyana.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 35 minutes 16 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 16 minutes 41 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com