Home Labarai NMDPRA tayi barazana ga gidajen Man Nijeriya

NMDPRA tayi barazana ga gidajen Man Nijeriya

Hukumar kula da harkoki sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya, (NMDPRA) ta yi barazanar ƙwace lasisin gidajen mai da ‘yan kasuwar da aka samu da laifin ɓoye man fetur don sayar wa ‘yan bumburutu.

Babban daraktan hukumar, Ogbugo Ukoha ne ya bayyana haka cikin wani bidiyo da hukumar ta wallafa a shafinta na X, lokacin wata ziyarar bazata da wata tawagar hukumar ta kai wasu gidajen mai a Abuja babban birnin ƙasar.

A ‘yan kwanakin baya-bayan nan ana fuskantar ƙarancin man fetur ɗin a wasu manyan birane da jihohin ƙasar.

A wasu jihohi, musamman da ke yankin arewacin ƙasar, ana fuskantar ƙarancin man, lamarin da ya tilasta wa wasu gidajen mai da dama rufewa, abinda kuma ya haifar da dogayen layuka a gidajen man da ke bayar da man.

Hukumar ta kuma ce sayar wa ‘yan bumburutun man a jarakuna saɓa doka ne tare, sannan kuma hakan na haifar da barazana ga kariyar muhalli.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp