Sayarwa ‘yan Bunburutu man fetur saba doka ce -NMDPRA

Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya, (NMDPRA) ta yi barazanar ƙwace lasisin gidajen mai da ‘yan kasuwar da aka samu da laifin ɓoye man fetur don sayar wa ‘yan bumburutu.

Babban daraktan hukumar, Ogbugo Ukoha ne ya bayyana haka cikin wani bidiyo da hukumar ta wallafa a shafinta na X, lokacin wata ziyarar bazata da wata tawagar hukumar ta kai wasu gidajen mai a Abuja babban birnin ƙasar.

A ‘yan kwanakin baya-bayan nan ana fuskantar ƙarancin man fetur ɗin a wasu manyan birane da jihohin ƙasar.

A wasu jihohi, musamman da ke yankin arewacin ƙasar, ana fuskantar ƙarancin man, lamarin da ya tilasta wa wasu gidajen mai da dama rufewa, abinda kuma ya haifar da dogayen layuka a gidajen man da ke bayar da man.

Hukumar ta kuma ce sayar wa ‘yan bumburutun man a jarakuna saɓa doka ne tare, sannan kuma hakan na haifar da barazana ga kariyar muhalli.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 11 minutes 21 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 10 hours 52 minutes 46 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com