Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya NLC, ta yi gargaɗi tare da yin barazanar fara yajin aikin sai baba-ta-gani, idan har aka kama shugabanta, Joe Ajaero.
Ƙungiyar ta yanke wannan shawarar ne a wani taron gaggawa da jagororinta suka gudanar a yau, Talata.
Taron ya gudana ne bayan gayyatar da rundunar ƴansandan Najeriya ta yi wa shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero, wanda ta ce hakan na da alaƙa ne da bincikensa da ake yi kan zargin samar da kuɗade domin tallafa wa ayyukan ta’addanci, da aikata laifuffuka ta shafukan intanet, da zamba, da haɗa baki wajen aikata laifuka da kuma cin amanar ƙasa.
Sai dai a nata ɓangaren, NLC ta bayyana zarge-zargen a matsayin marasa tushe kuma ta yi zargin cewa lamarin na da alaƙa da siyasa.
Ƙungiyar ƙwadagon ta zargi mahukuntan Najeriya da yunƙurin tursasawa da kuma musguna wa shugabanninta.
Ta kuma ce ana ƙoƙari ne wajen ganin an raunana ta bisa ‘fafutikar da take ta kare manufofin dimokuradiyya da haƙƙokin ma’aikatan Najeriya’.
Saboda haka ne jagororin ƙungiyar suka umarci dukkanin ɓangarorin ƙungiyar su fara haɗa kan mambobinsu a faɗin ƙasar da gargaɗin cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar dukkan matakan da suka dace, waɗanda suka haɗa da zanga-zanga da kuma dakatar da komai a ƙasar don kare mutunci da ƴancin kai na ƙungiyar.
“Idan har wani abu ya faru da shugabanmu, ko kuma aka kama shi, to za mu fara yajin aikin sai baba ta gani a faɗin ƙasar daga tsakar dare.” in ji NLC.
NLC na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ƙwadago mafiya ƙarfin faɗa a ji a Najeriya, wadda a lokuta da dama ta jagoranci ma’aikata domin nuna rashin amincewa da wasu manufofin gwamnati.
Ko a wannan shekara ta 2024, ƙungiyar ta shiga yajin aiki tare da gudanar da zanga-zanga bayan zargin gwamnati da rashin mayar da hankali a batun ƙarin albashin ma’aikata.
Hakan ya tursasa wa gwamnatin ƙasar sake kiran ƙungiyar zuwa teburin shawarwari, inda daga ƙarshe aka cimma matsayar nunka albashin ma’aikata daga naira 30,000 zuwa naira 70,000.
Sai dai daga baya an ga alamu na rashin jituwa tsakanin ɓangarorin biyu bayan da ƙungiyar ta NLC ta ce ba za ta janye daga zanga-zangar matsin rayuwa da aka gudanar a ƙasar ba kasancewar ba ita ce ta shirya ta ba.
Jim kaɗan bayan hakan ne wasu jami’an tsaro suka kai samame a babban ofishin ƙungiyar da ke Abuja, sai dai bayan koken da ƙungiyar ta yi, rundunar ƴansandan Najeriya ta ce ta kai samamen ne domin gano wasu muhimman takardu waɗanda za su zamo shaida a binciken da ake yi kan wani mutum, wanda ‘ke da hatsari’ ga ƙasar.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 48 minutes 0 second,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 29 minutes 25 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com