Home Labarai ‘Yan sanda sun kama bata gari 41 a jihar Kano

‘Yan sanda sun kama bata gari 41 a jihar Kano

Rundunar Yan Sandan jihar Kano, ta kama mutane 41 da ake Zargi da addabar jama’a, sassan jihar.

Wannan ya biyo bayan rahotannin da Rundunar Yan Sandan ta samu kan yadda batagarin suke zama tare da addabar mutane.

Mai magana da yawun Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa kwamishinan yan Sandan jahar CP Salman Dogo Garba, ya bayar umarnin shiga wuraren tare kama mutane 41 da kuma makamai da kayan maye da aka samu a wajensu.

Kwamishinan yan Sandan ya godewa al’ummar jahar Kano, bisa hadin kan da suke bayarwa domin duk irin wani laifi da ake aikata wa a jahar Yana raguwa.

Kiyawa, ya kara da cewa daman tuni babban sufeton Yan Sandan Nijeriya Kayode Adeolu Egbetokun, ya bayar da umarnin Fadada Sintiri da kuma tabbatar da amfani da bayanan sirri domin inganta tsaro.

Rundunar Yan Sandan jihar Kano karkashin jagorancin CP Salman Dogo Garba, ta yi babbar nasarar magance matsaloli na tsaro, Inda aka gudanar da Sintiri a lungu da sako na kwaryar birnin Kano, tare da Kai sumame a wuraren da ake Zargin batagarin matasa suna aika-aika a wuraren.

Sumamen ya Kai ga cafke mutane 41 da makamai da kuma kayan mayen da suke sha suna buguwa.

Wannan ya biyo bayan dagewar da Rundunar Yan Sandan ta yi, domin ganin an tabbatar da tsaro a Kano gaba daya.

Haka zalika Rundunar Yan Sandan ta kara godewa al’umma , saboda an samu raguwar aikata laifuka a wannan lokaci da ake ciki.

CP Dogo Garba, ya tabbatar wa da al’umma cewa za su ci gaba da zage damtse na tabbatar da tsaro da kare rayuka, lafiya da kuma dukiyoyon su.

A karshe Rundunar ta Yi kiran a ci gaba da ba wa Rundunar Yan Sandan jahar Kano, hadin Kai domin ci gaba da tabbatar da tsaro da zaman lafiya, Inda rundunar ta bayar da nambobin Waya don sanar da ita wani motsi ko wani Abu da ba a amince da shi ba ko agajin gaggawa.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp