Hukumomi a Jamhuriyar Nijar, na gudanar da bincike kan wasu mutane biyu da ake zargin sun kamu da cutar ƙyandar biri a yankin Zinder.
Read Also:
Babban magatakarda a ma’aikatar lafiyar Nijar Dakta Malam Ekoye Saidou wanda ya tabbatar da matakin cikin wata sanarwa ranar Laraba, ya buƙaci masu ruwa da tsaki a kowane mataki da su ƙarfafa matakan taka tsantsan a duk wuraren kiwon lafiya na gwamnati da masu zaman kansu da kan iyakoki.
Sanarwar tace ɗaukar matakin ya zama dole, sakamakon yadda cutar ta fara yaɗuwa zuwa yammacin Afirka.
Daga ranar 14 ga watan Agusta, mutane 833 ne suka kamu da cutar, ciki har da 9 da su ka mutu a yankin, wato 11 a Najeriya, 1 Ivory Coast da kuma 3 a Benin.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1240 days 7 hours 34 minutes 24 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1222 days 9 hours 15 minutes 49 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com