Tinubu na neman mallaka wa kansa Nijeriya – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya zargi shugaban ƙasar, Bola Tinubu da ‘neman mayar da Najeriya mallakin kansa’.

Atiku, ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023 ya yi iƙirarin cewa Tinubu yana jinginar da makoman matasan Nijeriya ga kansa da iyalinsa da kuma abokansa na kusa.

Atiku ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe ya fitar a ranar Laraba, inda ya bayyana damuwar sa kan cewa ko bayan Tinubu ya bar mulki, “zai yi wahala a warware abubuwan da ya kafa tare da kuma magance waɗannan matsalolin.”

Atiku ya yi zargin cewa Tinubu na saƙala harkokin kasuwancinsa cikin harkokin gwamnati a Legas, tare da cewar irin hakan ne ke faruwa a yanzu a matakin tarayya.

Atiku ya ce a sanarwar “na yi matuƙar mamaki da gano cewa kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya sanya ayyukansa na sayar da kayayyaki a ƙarƙashin kulawar OVH, wani kamfanin da Oando ke MALLAKIN kashi 49 cikin ɗari.”

“Oando fa yana ƙarkashin jagorancin Wale Tinubu ne, ƙanen Shugaban Tinubu.” in ji sanarwar.

Atiku ya bayyana baƙin cikinsa kan yadda a cewarsa “wasu kamfanoni da ke da kusanci da Tinubu suka dabaibaye harkokin kamfanin NNPCL ba bisa ka’ida ba.”

A wani sakon da ya wallafa a shafin sa na X a ranar Litinin, Atiku ya soki gwamnatin Tinubu kan cire tallafin man fetur wanda shi ne tushen halin da ƴan Najeriya ke ciki.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1255 days 5 hours 12 minutes 47 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1237 days 6 hours 54 minutes 12 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com