Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya rantsar da Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin mai riƙon muƙamin Babbar mai Shari’a ta Najeriya, kafin Majalisar Dattijan ƙasar ta tabbatar da naɗin nata.
Shugaban ya rantsar da ita ne a ranar Juma’a bayan dawowarsa daga Faransa.
Mai shari’a Kekere-Ekun za ta maye gurbin Mai shari’a Olukayode Ariwoola, wanda ya yi ritaya bayan ya kai shekara 70 a duniya.
A ƙa’idar Kotun Ƙolin, babban alƙali mai biye da shi ne zai maye gurbinsa, wanda hakan ya sa Mai shari’a Kudirat ce za ta maye gurbin da zai bari.