Ambaliya-Mutane sama da dubu 40 sun rasa muhallansu a Nijeriya

Aƙalla mutum 49 ne suka mutu a Najeriya sakamakon mamakon ruwan sama da ya haddasa ambaliyar a jihohin arewa maso gabashin ƙasar, a cewar hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa.

Kakakin hukumar Manzo Ezekiel, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa a da ya fitar ranar Litinin cewa jihohin Adamawa da Taraba na yankin ne da kuma Jigawa lamarin ya fi shafa, inda mutum sama da 41,344 suka rasa muhallansu.

A shekarar 2022, Najeriya ta fuskanci ambaliyar mafi muni cikin shekara 10, wadda ta yi ajalin mutum aƙalla 600, sannan ta raba miliyan 1.4 da muhallansu tare da lalata jimillar gonaki masu faɗin hekta 440,000.

“Yanzu ne muke shiga ƙololuwar damina, musamman a arewaci kuma lamarin ya tsananta,” a cewar sanarwar.

Zuwa yanzu ruwan ya lalata gonalki masu faɗin hekta 693 yayin da Najeriya ke fama da hauhawar farashin kayayyaki musamman na abinci.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 18 hours 39 minutes 3 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 20 minutes 28 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com