Home Labarai Ranar Hausa – Ko kun san wanda ya samar da bikin ranar...

Ranar Hausa – Ko kun san wanda ya samar da bikin ranar Hausa?

Karo na 10 kenan da ake gudanar da bikin ranar hausa ta duniya dukkan shekara, an shirya bikin ne domin kara fadada harshen a duniya da kuma kara samun kyakkyawar alaka tsakanin Hausawa da abokan zaman su.

A hannu guda akan yi amfani da ranar wajen kara tunatar da juna hanyoyin da ya kamata abi domin fidda A’I daga rogo, daga matsalolin dake addabar su kama daga tsaro, hadin kai da dai sauransu.

Albarkacin wannan rana PRNigeria ta tattaunawa da wanda ya fara kawo shawarar gudanar da bikin ranar hausa. Abdulbaki Jari, Dan Jarida ne dake Aiki da kafar yada labarai ta TRT Africa dake Turkiyya.

Inda yace an fara samar da wannan rana ne a shafin Twitter wanda yanzu ya koma X, da zummar dawo da hankalin al’umma wajen nemo bakin zaren matsalolin dake addabar su.

“Ranar hausa ta samo asali a shafin twitter wanda yanzu ya koma shafin X, mun fara wannan biki ne a ranar 26 ga watan Agustan 2015, a lokacin nazo da shawarar cewa ya kamata yadda muke da yawa mu ware wata rana da zamu rinka tattaunawa da harshen hausa domin tunatar da juna tasirin harshe  da kuma al’ada da kuma abu mafi muhimmaci wanda shine hadin kai.

Yace sun dauki wannan mataki ne kan yadda suka ga ana zuwa shafin sada zumunta ana fada ana tattauna wasu batutuwa da basu da muhimmanci, mai ma kon tattauna masu muhimmanci.

“Maimakon ya zama ana amfani da shafukan ana wayar da kai da zummar ganin cewa an nema maganin wadannan matsalolin musamman ta hanyar ankarar da shuwagabanni”

“Allah cikin ikon shi da aka yi wannan kira mutane sun amsa kiran inda wasu suka zo da shawarwari, wasu kuma suka zo da raha da sauransu ana kawo Karin Magana, wanda suma dai akwai hikima cikin Karin maganar, don kamar yadda muka sani ko wacce Karin Magana akwai hikima a ciki.

Taken bikin ranar hausan na bana dai shine, “tsintsiya madaurinki daya” hada kai domin inganta tattalin arziki da samar da zaman lafiya da tsaro.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Darakta Janar na NITDA ya yi Kira da a Hada Hannu Kan Tsarin AI a Taron Manyan ShugabanniƳancin Sanin Gaskiya: Bayani Game da Tsarin Gudanar da Harkokin Sadarwa na Najeriya Daga Franklyn Ginger-EkeHOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da Wiwi
X whatsapp