Rundunar tsaron Al’umma da adana kadarorin gwamnati wato civil defence ta hannata wasu daga cikin kayan da ta kama a hannun wasu matasa, lokacin zanga-zangar lumana a nan Kano, ga hukumar sadarwa ta kasa.
Kayan da rundunar ta hannata sun hada da na’ura mai kwakwalwa wato, Computer, Kujeru, Naurar sanyaya daki wato AC da dai sauran kayayyaki na miliyoyin nairori, da rundunar ta kama.
Read Also:
Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta bakin kakakin rundunar shiyyar Kano wato SC Ibrahim Idris Abdullahi.
Idan za a iya tunawa a ranar 10 ga watan Augustan da muke bankwana da shi, wasu matasa sun kutsa kai cikin Sabon ofishin hukumar sadarwa ta kasa dake sakatariyar Audu Bako, inda suka kwashe kayan dake ciki, da sunan zanga-zangar tsadar Rayuwa.
Yanzu haka dai jami’in hukumar sadarwa ta kasa shiyyar Kano ta karbi kayan ta hannun jami’inta wato Aminu Sulaiman Birnin Chido, inda a karshe ya yabawa rundunar tsaron Al’umma ta NSCDC bisa wannan kokari da suka yi.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 57 minutes 21 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 38 minutes 46 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com