Home General Hukumar KANSIEC ta sauya ranar zabe a jihar Kano

Hukumar KANSIEC ta sauya ranar zabe a jihar Kano

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano, KANSIEC ta sanar da sauya ranar gudanar da zaben kananan hukumomi zuwa 26 ga watan Oktoba.

shugaban hukumar, Farfesa Sani Lawan Malumfashi, ne ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai daya gudana ranar Juma’a a Kano, inda ya ce hukumar ta dauki wannan matakin ne duba da hukuncin da kotun koli ta yi na bai wa kananan hukumomi ‘yanci.

Tun da fari dai hukumar ta sanka ranar 30 ga watan Nuwamba domin gudanar da zaben.

Malumfashi, ya ce bisa gyaran da aka yi, a yanzu za a fara yakin neman zabe daga 1 ga watan Satumba zuwa karfe 12 na daren 26 ga watan Oktoba.

Sannan ya kara da cewa za a gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyu daga 3 ga watan Satumba zuwa 26 ga watan. haka kuma za a sanar da sakamakon zabe a ranar Lahadi 27 ga watan Oktoba.

daga bisani yace hukumar ta ware ranar 9 ga watan Nuwamba domin zaben cike gurbi idan akwai bukatar hakan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp