Home General Akwai yiwuwar za’a fuskanci matsalar karancin abinci a Nijeriya

Akwai yiwuwar za’a fuskanci matsalar karancin abinci a Nijeriya

Nijeriya na ci gaba da fama da matsalar karancin abinci, yayin da sabbin bayanai daga cibiyar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEOC) suka nuna cewa ambaliyar ruwa ta lalata gonaki sama da kadada 115,000 a faɗin ƙasar.

Jihohi 29 da ƙananan hukumomi 154 ne abin ya shafa, inda sama da mutum 611,000 lamarin ya shafa kai tsaye, mutum 225,169 suka rasa matsugunansu, gidaje 83,457 ne suka lalace, mutum 201 ne kuma suka rasa rayukansu sannan mutum 2,119 kuma suka samu raunuka a bana.

Wannan bayanin na ambaliya ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da ƙarancin abinci da kuma ƙaruwar hauhawar farashin kayan abincin, wanda hukumar kididdiga ta Najeriyan (NBS) ta bayyana ya hau sama da kashi 40 cikin 100.

Wani sabon bincike da babban bankin Najeriya CBN ya gudanar daga ranar 22 zuwa 26 ga Yulin 2024 ya nuna cewa, hauhawar farashin kayayyaki zai tilastawa magidanta a Najeriya kashe mafi yawan kuɗaɗen shigarsu kan abinci nan da watanni shida masu zuwa.

Al’umma Nijeriya dai na cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa, tun kafin da kuma bayan darewar shugaba Tinubu, abinda mahukunta a kasar ke alakantawa da halin ko in kula da gwamnatinda ta gaba ta yi da tattalin arzikin kasar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp