Ba a biyan haraji yadda ya kamata a Najeriya – Bill Gates

Hamshaƙin attajirin nan na Amurka, Bill Gates ya ce ba a karɓar haraji yadda ya kamata a Najeriya.

Yayin da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki kan abinci mai gina jiki da wata ƙungiyar matasan Afirka ta shirya a Abuja, shugaban gidauniyar Bill and Melinda Gates, ya ce nan da wani lokaci mai zuwa, Najeriya na iya zama babbar ƙasar da ke fitar da abinci zuwa kasuwannin duniya .

“A fannin noma, a yau Najeriya na ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke sayo abinci daga ƙetare, amma duba da yawan jama’ar ƙasar idan ƙasar ta yi amfani da shawarwarin da ake bai wa manoman ƙasar, to akwai yiwuwar ƙasar za ta samu bunƙasa a fannin samar da abinci, ta yadda ma za ta zama babbar mai fitar a abinci a duniya”, in ji shi.

Hamshaƙain attajirin ya kuma ce ya kamata manoman ƙasar su rungumi hanyoyin noma na zamani tare da amfani da irin shuka mai inganci domin samun bunƙasar noman abinci a ƙasar.

Haka kuma ya yi kira ga gwamnatin ƙasar ta bunƙasa fannin lafiyarta.

“Ya kamata a bai wa fannin lafiya fifiko. Gwamnatin ƙasar ta jima tana yin shirin ɗaukar nauyin fannin lafiyar fiye da yadda yake a yanzu. To sai dai a haƙiƙanin gaskiya a Najeriya ba a biyan haraji yadda ya kamata”.

Bill Gates ya ce duk ‘yan ƙasar da ke son ilimi da lafiyarsu do ya wajaba a kansu su riƙa sauke haƙƙokin da ke kansu.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 21 hours 55 minutes 59 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 37 minutes 24 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com