Ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP ta buƙaci jami’an tsaron Nijeriya su ɗauki mataki kan ‘barazanar’ da suka ce Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi musu.
A ƙarshen makon a ya gabata ne dai tsohon gwamnan na jihar Rivers ya yi barazanar haifar da rikicin siyasa a jihohin gwamnonin jam’iyyar, matsawar suka ci gaba da sa baki kan rikicin siyasar jihar Rivers.
”Na ji wasu gwamnoni da suka ce za su ƙwace jam’iyyarmu don miƙa wa wani, Ina tausaya wa waɗannan gwamnoni, saboda zan kunno musu wutar da ba za su iya kashe ta ba a jihohinsu”, in ji Mista Wike.
To sai dai cikin sanarwar da daraktan ƙungiyar gwamnonin PDPn, Emmanuel Agbo, ya fitar ƙungiyar ta ce babu wanda ya fi ƙarfin doka sannan ta buƙaci jami’an tsaro su ɗauki mataki kan kalaman ministan, kamar yadda gidan Talbijin na Channels ya ruwaito.
“Ƙungiyarmu na kira da shugabannin hukumomin tsaro na ƙasar nan su ɗauki mataki kan kalaman ministan da ke barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da ƙoƙarin haifar da fiitina a jihohin, saboda babu wanda ya fi ƙarfin doka”, in ji sanarwar.
Gwamnonin na PDP sun kuma ce kalaman na mista Wike ba abu ne da za a lamunta ba saboda yadda suke barazana ga zaman lafiyar ƙasa.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 16 minutes 59 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 58 minutes 24 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com